Kwallon Kafa - 
Wallafa labari : Litinin 13 Agusta 2012 - Bugawa ta karshe : Litinin 13 Agusta 2012

Bayern da Juventus sun lashe Super Cup, City ta lashe Community Shield

Jagoran 'Yan wasan Manchester City Vincent Kompany ya daga karkuwar Ingila da suka lashe bayan lallasa Chelsea
Jagoran 'Yan wasan Manchester City Vincent Kompany ya daga karkuwar Ingila da suka lashe bayan lallasa Chelsea
REUTERS/Nigel Roddis

Daga Awwal Ahmad Janyau

Kungiyar Bayern Munich ta lashe kofin Jamus na Super Cup bayan doke Borussia Dortmund ci 2-1. A Italiya, kungiyar Juventus ce ta lashe Super Cup bayan samun sa’ar Napoli. A Ingila kuma Manchester City ce ta lashe Community Shield bayan lallasa Chelsea ci 3-1.

Gab da fara wasa ne Bayern Munich ta zira kwallaye biyu a raga ana minti 11 da fara wasa. Ana kusan kammala wasa ne dan wasan Borussia Dortmund Robert Lewandowski ya zira kwallo daya.

A Italia kuma kungiyar Juventus ce ta lashe Super Cup bayan samun sa’ar Napoli. An dai kammala wasan ne ana ci 2-2. Amma bayan shiga lokuttan da aka kara ne Juventus ta samu sa’ar lashe wasan sanadiyar kwallon da dan wasan Napoli ya zira a ragarsu.

A Ingila kuma Manchester City ce ta lashe Community Shield bayan lallasa Chelsea ci 3-1.
Hakan kuma ke nuna Roberto Mancini ya shirya tsab domin kare kambun Premier da City zata fara bugawa a karshen makon gobe.

Fernando Torres ne dai ya fara zira kwallo a ragar City kafin Alkalin wasa ya ba Ivanovic jan kati. City ta samu barke kwallon ne ta kafar Yaya Toure, daga nan kuma Tevez da Samir Nasri suka sake zira wasu kwallyen biyu a raga.

Wannan na zuwa ne kuma a dai dai lokacin da Manchester City ke kammala cinikin Jack Rodwell daga Everton, amma babu wani bayani game da kudin cinikin dan wasan.
 

tags: Bundesliga - Kwallon Kafa - Premier League - Seria A
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Close