Isa ga babban shafi

Britaniya ta goyi bayan ayyukan mujallar Charlie Hebdo

Fraiministan Birtaniya David Cameron ya kare damar yancin fadin albarkacin bakin da mujallar Charlie Hebdo ke anfani da shi wajen cin zarafin addinai, a matsayin martani ga kalaman Fafaroma Francis.Cameron wanda ke ziyarar kasar Amurka yace suna cikin jama’a ne masu ‘yancin fadin albarkacin baki, saboda haka akwai damar sukar addinan jama’a.Firaministan yace a matsayin sa na kirista, idan ka soki Annabi Isa Alaihis Salam, zai ji zafi amma kuma saboda yancin fadin albarkacin baki babu abinda zai iya yi dan ramako.Cameron yace ya zama wajibi jama’a su fahimci cewar jaridu da mujallau na iya wallafa abinda suke so muddin basu karya doka ba.Shi dai Fafaroma Francis yayi suka ne kan yadda yan bindiga suka afkawa ma’aikatan mujallar Charlie Hebdo a Faransa, kana yace ba dai dai bane a dinga cin zarafin wani addini.Fafaroma ya kara da cewar a matsayin sa na shugaban mabiya darikar Katolika, wanda ya zagi mahaifiyar sa lalle zai naushe shi. 

Wani mutum dake nuna goyon baya ga mujallar Charlie Hebdo
Wani mutum dake nuna goyon baya ga mujallar Charlie Hebdo REUTERS/Darrin
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.