Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

MH17: Rasha ta kalubalanci Amurka

Gwamnatin kasar Rasha ta kalubalanci Amurka akan ta fitar da hujjoji game da zargin an yi amfani da makami mai linzami aka harbo Jirgin Malaysia da ya tarwatse a yankin da ‘Yan a ware ke iko a kasar Ukraine. Mataimakin Ministan Tsaron Rasha Anatoly Antonov ya kalubalanci Amurka ta fito da hujjojin da tace tana da su akan an yi amfani da makami mai linzami daga gabacin Ukraine.

'Yan tawayen Ukraine sun tsaya a inda Jirgin Malaysia ya fadi a yankin Donetsk.
'Yan tawayen Ukraine sun tsaya a inda Jirgin Malaysia ya fadi a yankin Donetsk. Reuters/Maxim Zmeyev
Talla

Tuni, Amurka tace tana da bayanai na hujjoji da ta samu daga tauraron Dan Adama da suka nuna an yi amfani da makami mai Linzami aka harbo Jirgin Malaysia a ranar Alhamis din mako jiya inda dukkanin mutanen Jirgin suka mutu.

Kuma Amurka ta yi zargin cewa kasar Rasha ce ta ba ‘Yan tawayen Ukraine makamai domin yaki da gwamnatin Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.