Isa ga babban shafi
Amnesty

Amnesty ta soki kasashen duniya

Kungiyar Kare hakkin Bil’aAdama ta Amnesty International ta soki kasashen duniya kan yadda suke zuba ido suna kallon wasu kasashe da kungiyoyin ‘Yan ta’adda suna cin zarafin mutane ba tare da daukar matakai ba.

Genevieve Garrigos, Jagorar kungiyar Amnesty International a Faransa
Genevieve Garrigos, Jagorar kungiyar Amnesty International a Faransa © Xavier de Torres
Talla

Rahotan Kungiyar na 2014 da ta fitar a yau Laraba, ya yi nazari ne kan kasashe 160 da suka kunshi 23 a Afirtka ta tsakiya da Afirka ta Yamma.

Kungiyar ta bukaci daukar matakin gaggawa don kawo karshen matsalar da ta bayyana abin kungiya ne.

Rahotan kungiyar ya yi nuni da yadda miliyoyin jama’a suka shiga tsaka mai wuya sakamakon tashin hankalin da suka gani ko kuma ya ritsa da su, wanda kasashen duniya suka nade hannunsu ba tare da daukar mataki ba.

Kungiyar ta yi nazari kan yadda ake cin zarafin Bil Adama, da kuma yadda ma su aikata laifukan ke cin Karensu ba babbaka.

Amnesty ta ce Majalisar Dinkin Duniya da aka kafa bayan yakin duniya na biyu domin kaucewa sake aukuwar tashin hankali, ta kasa magance tashe-tashen hankulan da ake gani yau, wadanda ke haifar da miliyoyin ‘yan gudun hijira.

Kungiyar ta zargi kungiyoyi irinsu ISIS da Boko Haram da Mayakan al Qaeda reshen Magreb da Seleka da anti Balaka na Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya a matsayin masu aikata ta’adanci da zub da jinin wadanda ba su ji ba su gani ba, inda ta bukaci kasashen duniya su tashi tsaye don daukar mataki akansu.

Amnesty ta zargi Majalisar Dinkin Duniya da kasa magance matsalolin da ake fuskanta a kasashen Iraqi da Syria da Gaza da Isra’ila da Ukraine.

Kungiyar ta kuma zargi kasashe irinsu Amurka da China da Canada da India da Isra’ila da Rasha da kin sanya hannu kan yarjejeniyar sayar da makamai, matakin da ke ba su damar sayar da makaman da ake cin zarafin Bil Adama da su, musamman  yadda ake tura makamai zuwa Iraqi da Isra’ila da Rasha da Sudan ta kudu da Syria wadanda a karshe suke fadawa hannun yan ta’adda.

kungiyar ta ce gwamnatoci sun kasa kare hakkin Bil Adama a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.