Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta nuna barnar Boko Haram a Baga

Manyan Kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda biyu na dunya sun nuna hutunan da ke nuna barnar da Boko Haram ta yi a garin Baga da Doron Baga da ke cikin Jihar Borno a yankin arewa maso gabacin Najeriya.

hoton tauraron Dan Adam da ke nuna ta'adin da Boko Haram ta yi a Baga da Doron Baga
hoton tauraron Dan Adam da ke nuna ta'adin da Boko Haram ta yi a Baga da Doron Baga AFP PHOTO / DIGITALGLOBE / AMNESTY INTERNATIONAL
Talla

Hotunan da Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty da Human Right Watch suka dauka a tauraron dan adam bayan Boko Haram ta kai hare hare a Baga da Doron Baga sun tabbatar da cewa mutane da dama ne aka kashe.

Amnesty tace daruruwan mutane ne aka kashe yawancinsu mata cikinsu har da wata mata da ke nakuda da yara kanana da dama.

Amnesty tace Matar da ke nakuda ta mutu bayan rabin jikin Jaririnta ya fito.

Amnesty da HRW sun ce daruruwan mutane ne aka kashe tare da yin watsi da ikirarin Sojin Najeriya da suka ce mutane 150 ne aka kashe, sabanin mutane 2000 da mutanen yankin suka ce sun mutu.

Hotunan da Amnesty ta nuna tace an lalata jimillar gidaje 3,100 a Doron Baga, 620 a garin Gaba.

Akalla Gidaje 16 aka kona kurmus a Baga yayin da kuma mutane kimanin 20,000 suka kauracewa garin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.