Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojoji sun ce Mutane 150 aka kashe a Baga

Ma’aikatar Tsaron Najeriya tace mutane 150 kawai aka kashe a garin Baga na Jihar Borno ba 2,000 ba kamar yada kafofin yada labarai suka ruwaito. Mai magana da yawun rundunar Sojin kasar Janar Chris Olukolade ya yi watsi da rahotannin da suka ce mutane 2000 aka kashe a Baga.

Gidajen Garin Gamboru Ngala da Boko Haram ta kona a Jihar Borno a Najeriya.
Gidajen Garin Gamboru Ngala da Boko Haram ta kona a Jihar Borno a Najeriya. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Sai dai wasu rahotanni daga wadanda suka gudu daga garin sun ce har yanzu gawawaki na can yashe a garin an rasa ma su binne su.

Mutane da dama ne Boko Haram ta kashe yawancinsu mata da yara kanana a harin da mayakan kungiyar suka kaddamar a garin Baga.

Dubban mutanen Baga ne suka fice garin zuwa kasar Chadi da ke makwabtaka da Najeriya bayan da 'Yan Boko Haram suka kona gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.