Isa ga babban shafi

Napoli ta sallami kocinta Walter Mazzarri, ta maye gurbinsa da Calzona

Kungiyyar kwallon kafa ta Napoli ta sallami kocinta, Walter Mazzarri Bayan shafe watanni 3 kacal yana aiki, kana ta maye gurbinsa da kocin Slovakia, Francesco Calzona.

Tsohon kocin Napoli, Walter Mazzarri.
Tsohon kocin Napoli, Walter Mazzarri. © afp
Talla

A watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne Mazzarri ya karbi aiki daga hannun Rudy Garcia, kuma yanzu ya bar kungiyar tana matsayi na 9 a gasar Serie A ta kasar Italiya.

Rahotanni daga Italiyar na cewa Calzona ya sanya hannu a kwantiragin da zai yi aiki har zuwa karshen wannan kaka ne, kuma duk da haka zai ci gaba da horar da tawagar kwallon kafar kasar Slovakia.

Mai kungiyar ta Napoli, Aurelio de Laurentiis ya ce ya gode wa Mazzarri saboda gudummawa da ya bai wa kungiyar a locakcin da take cikin kalubale.

A ranar Laraba, Napoli za ta karbi bakkuncin Barcelona a zagayen kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai, zubi na farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.