Isa ga babban shafi

Napoli ta yi watsi da batun neman yafiyar Osimhen bayan bidiyon tsokana

Kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta ce ba ta da nufin batanci ko muzanta dan wasanta Victor Osimhen bayan bidiyon da ta sanya a shafinta na Tiktok da aka bayyana da tsokana ga dan wasan na Najeriya sakamakon barar da bugun fenaritin da ya yi a wasansu da Bologna.

Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen.
Dan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen. REUTERS - CIRO DE LUCA
Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar game da wannan batu, ta ce bata yi bidiyon da nufin muzanta Osimhen ba, a don haka ba za ta bayar da hakuri ko kuma neman yafiya akan hakan ba.

Bidiyon wanda tuni Napoli ta goge daga shafinta, ya nuna Osimhen lokacin da ya barar da bugun fenaritin yayinda aka sanya wata muryar tsokana a kasa da ke cewa ‘‘a bani bugun fenariti’’

Tuni dai dillalin Osimhen ya sha alwashin daukar matakin shari’a kan kungiyar sai dai mai horarwa Rudi Garcia ya ce Osimhen mai shekaru 24 dan wasa ne mai matukar muhimmanci ga Napoli kuma baza su yi kokarin muzanta shi ta kowacce fuska ba.

A cewar Gracia yadda Napoli ta kafe wajen kin sayar da Osimhen duk da tarin kungiyoyin da suka nuna sha’awar sayen shi manuniya ce ta muhimmancin dan wasan a kungiyar.

Bayanai dai na cewa wannan bidiyo ya matukar sosa zuciyar dan wasan na Najeriya lura da cewa hatta bayan nasarar shi da zura kwallo a wasan da Napoli ta lallasa Udinese da kwallaye 4 da 1 ya ki nuna murnar zura kwallon sai bayan da abokanan wasansa suka fara murna tukuna ya bi bayansu.

A shekarar 2020 ne Napoli ta sayo kan yuro miliyan 81.3 inda ya taimawa kungiyar wajen lashe kofin Serie A karon farko cikin shekaru 33 a kakar da ta gabata bayan zura kwallaye 26 a wasanni 32.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.