Isa ga babban shafi

Osimhen zai dauki matakin shari'a kan Napoli bayan yi masa shagube

Dillalin dan wasan Napoli Victor Osimhen wato Roberto Calenda ya yi barazanar daukar matakin shari’a kan kungiyar saboda cin zarafin dan wasan a shafinta na sada zumunta, bayan da dan wasan na Najeriya ya yi rashin nasara a bugun fenaritin da ya buga yayin wasan kungiyar da Bologna.

Victor Osimhen na Najeriya da ke taka leda da Napoli ta Italiya.
Victor Osimhen na Najeriya da ke taka leda da Napoli ta Italiya. REUTERS - JENNIFER LORENZINI
Talla

Napoli ta sanya bidiyon Osimhen lokacin da ya rasa bugun fenaritin tare da wata muryar tsokana a kasa da ke cewa ''ku bani bugun fenariti’’ yayinda a kasa kuma aka yi rubutun ''Mai kan kwakwa'' lamarin da ya ja hankali masu fashin baki da suka rika fassare-fassaren abinda kungiyar ta ke nufi.

Duk da yadda Napoli ta cire bidiyon tuntuni, amma sakon da Calenda ya wallafa a shafinsa na X da ka fi sani da Twitter ya ce dole ne su dau matakin shari’a kan kungiyar domin abin da aka aikatawa dan wasan ba abin karba ba ne.

A cewar Dillalin na Victor Osimhen kai tsaye wanna bidiyo zai shafi rayuwar dan wasan da kuma haddasa masa tsokana da yarfe a tsawon rayuwarshi ta kwallo.

Osimhen dan Najeriya da Napoli ta saya kan yuro miliyan 81.3 a 2020, ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofin Serie A karon farko cikin shekaru 33 bayan zura kwallaye 26 a wasannin lig 32.

Yanzu haka dai akwai jita-jitar da ke alakanta Osimhen dan shekaru 24 da Chelsea mai doka firimiya baya Manchester United ko da ya ke har yanzu Napoli ba ta ce komi kan jita-jitar ba.

Sai dai duk da wannan matsala dan wasan na Najeriya na cikin tawagar Napoli da za ta kara da Udinese yau Laraba, karkashin gasar Serie A da kungiyar ke rike da kambunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.