Isa ga babban shafi

Roma da kammala kulla yarjejeniyar karbar aron Lukaku daga Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Roma ta kammala kulla yarjejeniyar karbar aron Romelu Lukaku daga Chelsea wanda zai shafe tsawon kakar bana ya na takawa kungiyar mai doka gasar Serie A leda.

Romelu Lukaku ya isa Roma bayan kammala kulla yarjejeniyar karbar aron shi daga Chelsea.
Romelu Lukaku ya isa Roma bayan kammala kulla yarjejeniyar karbar aron shi daga Chelsea. AP - Alfredo Falcone
Talla

Roma karkashin jagorancin Jose Mourinho ta bi sahun manyan kungiyoyin Turai da suka mika bukatar karbar aron Lukaku ne bayan da Mauricio Pochettino ya bayyana cewa dan wasan baya sahun wadanda zai yi amfani da su a wannan kaka.

Lukaku dan Belgium mai shekaru 30 da kanshi ya zabi komawa Roma fiye da Inter Milan kungiyar da ya kai wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a bara, amma kuma suka yi rashin nasara a hannun Manchester City.

Wasu rahotanni sun ce gabanin komawa Roma a yau Alhamis, kungiyoyin Lig din Saudiya da dama sun tuntubu dan wasan na Belgium amma ya yi watsi da tayinsu.

Tuni dai Lukaku ya isa Roma inda ya samu tarba ta musamman daga dubunnan magoya bayan kungiyar da suka yi dafifin tarbar shi.

A jawabin da ya gabatar, Lukaku ya ce tarba da kaunar da kungiyar ta Roma ta nuna masa zai kara masa kwarin gwiwar bayar da gagarumar gudunmawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.