Isa ga babban shafi

CAF ta dakatar da kyaftin na tawagar kwallon kafar Mali a wasanni 4

Hukumar kwallon kafar Afrika CAF ta bai wa kyaftin na tawagar kwallon kafar kasar Mali, Hamari Traore horon dakatarwa na wasanni 4 bayan da aka same shi da laifin yi wa alkalin wasa tsageranci.

Kyaftin na Mali Hamari Traoré da dan wasan Afika ta KuduThapelo Maseko.
Kyaftin na Mali Hamari Traoré da dan wasan Afika ta KuduThapelo Maseko. © AFP / FADEL SENNA
Talla

An bai wa dan wasan bayan mai shekaru 32 jan kati ne bayan da aka kammala wasan daf da kusa da karshe wanda Mali ta yi rashin nasara a hannun Ivory Coast a gasar kofin nahiyar Afrika ta AFCON a ranar 3 ga watan Fabrairu.

Traore ya kalubalanci alkalin wasan dan kasar Masar, Mohamed Adel, inda suka yi ta cacar baki har sai da abokan wasansa ne ma suka janyo shi bayan da Eagles ta Mali din ta yi rashin nasara 2 da 1 a karin lokaci.

An ci tarar hukumar kwallon kafa ta kasar Mali dala dubu 10 saboda abin da aka kira halin tsageranci da suka nuna wa alkalin wasa, da rashin tawakkali a wasa, a yayin da aka ci tarar hukumar kwallon kafar Ivory Coast dala dubu 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.