Isa ga babban shafi

Tsawa ta sauka akan wani dan wasa a kasar Indonesia a yayin da ake tsakiyar wasan

Bari mu fara labarin wasanni da wani labari marar  dadi da yafaru a kasar Indonesia bayan ana tsakiyar buga wasa.

Tun bayan karbar ragamar jagorancin United da Ole Gunnar Solskjaer ya yi daga hannun Jose Mourinho, kungiyar ta samu nasara a wasanni 10, daga cikin jimillar wasanni 11
Tun bayan karbar ragamar jagorancin United da Ole Gunnar Solskjaer ya yi daga hannun Jose Mourinho, kungiyar ta samu nasara a wasanni 10, daga cikin jimillar wasanni 11 REUTERS/David Klein
Talla

Bari mu fara labarin wasanni da wani labari marar  dadi da yafaru a kasar Indonesia bayan ana tsakiyar buga wasa.

A wani mummunan yanayi a wasan kwallon kafa na kasar Indonesiar a ranar Asabar, yayin da tsawa ta fado kan  Septain Raharja, kuma daga baya ya mutu sakamakon raunin da ya samu.

Wani faifan bidiyo ya dauki ainihin lokacin da tsawar ta buge mutumin dan shekaru 35. Ya fadi a filin wasa na Siliwangi da ke Bandung a yammacin ranar Asabar.

Raharja na fafatawa ne a wasan sada zumunci tsakanin kungiyar FLO FC Bandung da FBI Subang, lokacin da tsawa ta fado a kan shi da misalin karfe 4:20 na yamma agogon kasar.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida PRFM News sun bayyana cewa a zahiri yana ci gaba da jan numfashi bayan  kuma an garzaya da shi asibitin yankin domin yi masa magani.

A nan kuwa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na cikin wani tashin hankali bayan da Real Madrid ta ke gabanta da maki 10 a gasar La Liga

Kocin na Barcelona Xavi yana fuskantar suka daga magoya bayan kungiyar akan rashin samun sakamako  da ya dace, a wasan da kungiyar ta buga a karshen mako da ta yi kunnen doki 3-3 da Granada, Barcelona na a mataki na 3 a kan teburin gasar La Liga da maki 51 cikin wasanni 24 da ta buga, ta yi nasara a wasanni 15 ta buga kunnen doki 3 sannan ta sha duka a wasanni 6.

A kwanan baya dai Xavi ya bayyana cewa a karshen kakar wasanni zai yi murabus daga mukamin sa na mai horaswa, duk da cewa ita  dai kungiyar akwai zaratan 'yan wasan ta da suke da rauni wanda ake ganin shi ne silar rashin samun nasarar da kungiyar keyi.

Rahotanni na cewa akwai yiwuwar za a iya sallamar Xavi daga mukaminnsa in har bai samu nasara akan wasan da zasu kara na zakarun turai waton Champons League da kungiyar Napoli ba.

Hukumar kwallon kafar kasar Argentina ta aike wa shahararren dan wasan ta Leonel Messi gayyatar buga ma ta gasar Olympique na shekara ta 2024 da kasar Faransa za ta karbi bakunci.

Nasarar da Argentina ta samu a wasan neman gurbin zuwa gasar Olympique da ta doke kasar Brazil da ci 1 da nema ne ya ba wa tawagar ta Argentina damar zuwa gasar, Leonel Messi yana cikin tawagar 'yan wasan da suka taimaka wa kasar sa wajen lashe kofin Duniya da kasar Qatar ta karbi bakuncin sa a shekara ta 2022, bayan da suka doke kasar Faransa a wasan karshe, ana sa rai wannan karon ma dan wasaan zai taimakawa kasar samun nasara a gasar ta Olympic.

A sakamakon wasannin da a kara a sauran League din Turai kuwa a gasar league din Ingila anyi wasa tsakanin kungiyar Crystal Palace da Chelsea inda suka tashi 1-3, sai dai Crystal Palace ce ta fara zura kwallo a ragar Chelsea a mintina na 30 ta hannun Lerma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a mintuna na 47 sai dan wasan  Conor Gallagher na chelsea ya farke kwallo 1 da kuma a mintina na 90 ya sake zura kawallo, chelsea dai na amatsayin na 10 a kan teburin league da maki 34 cikin wasanni 24 da ta buga.

A gasar league din serie A na kasar Italia ma an kece raini tsakanin Juventus da Udenese inda kungiyar Udenese ta samu nasara kan Juventus har gida da ci 1 mai ban haushi, Juventus dai na a mataki na 2 da maki 53 a cikin wasanni 24 da ta buga ta yi nasara a wasa 16 ta yi kunnen doki 5 ta kuma rasa wasanni 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.