Isa ga babban shafi
FIFA

Amnesty ta soki Qatar akan Lebarori

Kungiyar kare hakkin bila’adama ta Amnesty International ta soki kasar Qatar akan rashin cika alkawalin da ta dauka na inganta rayuwar bakin haure da ke lebaranci a sabbin filayen wasannin da ta ke ginawa domin karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2022.

Wani lebara yana hutuwa a wani gidan Lebarori a birnin Doha
Wani lebara yana hutuwa a wani gidan Lebarori a birnin Doha REUTERS
Talla

Amnesty ta bukaci FIFA ta shiga tsakani.

A cikin rahoton da Amnesty ta fitar ta bayyana damuwa akan yadda ake cin zarafin lebarori a Qatar na rashin biyansu kudaden da suka dace, tare da hanawa masu ficewa kasar.

Sai dai kuma kamfanonin da ke hulda da hukumar FIFA Coca Cola da kamfanin hada hadar kudi na Visa sun ce za su taimaka tare da matsa kaimi ga hukumar FIFA domin shiga tsakanin rikicin lebarori a Qatar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.