Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA na son a yi Qatar 2022 a lokacin hunturu

Kwamitin da FIFA ta kafa kan batun gasar cin kofin duniya a Qatar ya bukaci da gudanar da gasar a lokacin hunturu tsakanin watan Nuwamba zuwa Disemba sabanin watan Yuni da Yuli da ake matsanancin zafi a kasar.

Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA
Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA AFP PHOTO / FADEL SENNA
Talla

A cikin wata sanarwa da FIFA ta fitar tace kwamitin ya amince a gudanar da gasar a watan Nuwamba da Disemba a matsayin lokacin da ya dace a gudanar da gasar a Qatar a 2022.

Sai dai kuma a watan Maris ne Hukumar FIFA za ta yanke hukunci

Tuni dai sakataren FIFA Jerome ya tabbatar da cewa ba za a yi wasannin gasar cin kofin duniya ba a watanni Yuni da Yuli a Qatar duk da cewa bangaren Turai na korafi game da sauyin lokacin zai shafi wasanninsu.

Ana sa ran kungiyar gamayar Manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai za su fitar da nasu lokacin da suke tunanin ya dace a gudanar da wasannin a Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.