Isa ga babban shafi
Kamaru

Eto’o ya yi wa Kamaru Ritaya

Fitaccen dan wasan Kamaru Samuel Eto’o ya bayyana yin ritaya daga bugawa kasar shi wasa, wannan matakin kuma na zuwa ne bayan an karbe wa dan wasan mukaminsa na jagoran ‘Yan wasan Indomitable Lions. Dan wasan ya fitar da sanarwar yi wa Kamaru ritaya ne a shafin shi na Tweeter da Facebook yana mai godewa masoyansa na Afrika da duniya baki daya.

Samuel Eto'o na Kamaru
Samuel Eto'o na Kamaru REUTERS/David Gray
Talla

Eto’o ya bugawa Kamaru wasan karshe ne a gasar cin kofin duniya a Brazil. Amma zai ci gaba da taka kwallo a kungiyar Everton da ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da ita a Premier League.

Eto’o ya zirara wa Kamaru kwallaye 56 a wasanni 116 da ya bugawa kasar shi, sannan ya lashe kofin gasar cin kofin Afrika guda biyu da zinari a wasannin Olympics. Sannan ya karbi kyautar gwarzon Afrika har sau hudu.

Eto’o dai yana cikin zaratan ‘Yan wasan Afrika da tarihin kwallo a nahiyar ba zai ta ba mantawa da su ba saboda ficensa a Turai musamman rawar da ya taka a Barcelona kafin ya koma Intar Milan inda ya lashe kofunan gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.