Isa ga babban shafi
CAF

Eto’o ya sake sukar Mourinho

Samuel Eto’o na Kamaru ya sake mayarwa Mourinho na Chelsea da martani, inda ya kira shi da sunan dabba a wata zantawa da aka wallafa a shafin Intanet na hukumar CAF da ke kula da kwallon kafa a Afrika.

Samuel Eto'o na Kamaru
Samuel Eto'o na Kamaru
Talla

A watan Maris ne Mourinho ya yi tsegumi akan shekarun Eto’o, inda yace shekarun dan wasan sun haura 33 kamar yadda Eto’o ke ikirari a hukumance.

An dade kuma Eto’o bai ce uffan ba, amma a makon jiya dan wasan ya kira Mourinho da sunan wawa, sannan kuma a lokacin da ya ke zantawa da hukumar CAF game da shirye shiryen gasar cin kofin duniya ya Mourinho da sunan Kare.

A watan gobe ne kwangilar Eto’o zata kawo karshe, kuma dan wasan yace yana tunanin ci gaba rayuwa ne a Amurka ko kuma a gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.