Isa ga babban shafi
Brazil 2014

Neymar yana son Messi ya lashe kofin Duniya

Duk da adawar da ke tsakanin Brazil da Argentina a tarihin kwallon kafa amma Neymar na Brazil yace yana son Lionel Messi abokin wasan shi a Barcelona ya lashe kofin duniya a ranar Lahadi inda Argentina zata fafata da Jamus da ta caccasa Brazil ci 7 da 1.

Dan wasan Brazil Neymar yana kwance a gadon Asibiti
Dan wasan Brazil Neymar yana kwance a gadon Asibiti Foto: CBF
Talla

Neymar wanda ke jinya a Asibiti a lokacin da Jamus ta ba Brazil kashi a zagayen dab da na karshe yace ya dace Messi ya hada da kofin duniya a cikin jerin Kofunan da ya lashe a rayuwarsa.

A lokacin da Neymar ke zantawa da manema labarai yace yana yi wa Messi fatar alheri.

Akwai dai yiyuwar dubban mutanen Brazil zasu marawa Argentina baya domin su rama dukan da Jamus ta yi wa Brazil din a ranar Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.