Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Barcelona ta saye Suarez

Barcelona ta kammala cinikin Luis Suarez na Uruguay tsakaninta da Liverpool duk da hukuncin da dan wasan ke fuskanta akan cizon dan wasan Italiya Giorgio Chiellini a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Dan kasar Uruguay Luis Suarez sanye da rigar Kungiyar Liverpool
Dan kasar Uruguay Luis Suarez sanye da rigar Kungiyar Liverpool REUTERS/Phil Noble
Talla

A cikin wata sanarwa da Barcelona ta fitar a yau Juma’a tace ta cim ma yarjejeniya tsakaninta da Liverpool akan Suarez, amma ba tare da bayyana adadin kudin cinikin dan wasan ba.

Amma Jaridun kasar Spain sun ruwaito cewa Barcelona ta saye Suarez ne akan kudi euro Miliyan 80 amma Jaridun Birtaniya sun ce euro Miliyan 94 ne Barcelona ta saye Dan wasan.

Liverpool ta wallafa sakon Suarez a shafinta na Intanet,  yana yi wa magoya bayan kungiyar bankwana, tare da bayyana dalilan da ya sa ya amince ya koma Barcelona.

A makon gobe ne Suarez zai tafi Barcelona domin a diba lafiyarsa kafin ya sanya hannu akan yarjejeniyar shekaru biyar da kungiyar.

Wannan yarjejeniyar tsakanin Barcelona da Liverpool na zuwa ne bayan Arsenal ta kammala cinikin Alexis Sanchez daga Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.