Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Suarez: Barcelona ta fara tattaunawa da Liverpool

Rahotanni daga Ingila sun ce wakilan Barcelona sun gana da wakilan Liverpool game da Luis Suarez da aka hukunta saboda tabi’ar shi ta cizon ‘Yan wasa. Kodayake shugaban Barcelona bai bayar da haske ba akan bukatar da suke yi wa Suarez amma Wata majiya daga Anfield ta kwarmato cewa kafin fara tattaunar tsakanin bangarorin biyu, Liverpool ta tsaya tsayin daka akan ko za’a fara tattaunawar sai idan Barcelona zata biya kudi da suka kai fam Miliyan 70 zuwa 80.

Luis Suárez, na Liverpool
Luis Suárez, na Liverpool ©Reuters.
Talla

Barcelona na nazarin mikawa Liverpool Alex Sanchez tare da yin ciko kafin ta karbi Suarez, wanda duniya ta yaba ma shi bayan ya fito ya nemi gafara akan cizon da ya yi wa dan wasan Italiya a gasar cin kofin duniya a Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.