Isa ga babban shafi
CAF

Ahly ta lashe Kofin gasar Zakarun Afrika

Kungiyar Al Ahly ta Masar ta lashe kofin zakarun Nahiyar Afrika karo na bakwai bayan doke kungiyar Esperence ta Tunisia da jimillar kwallaye 3-2 a wasan karshe da aka gudanar a ranar Assabar.

'Yan wasan Al Ahly  na Masar suna murnar lashe kofin Zakarun Afrika bayan doke Espérance ta Tunisia (1-2),
'Yan wasan Al Ahly na Masar suna murnar lashe kofin Zakarun Afrika bayan doke Espérance ta Tunisia (1-2), REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

A wasan farko dai kungiyoyin biyu sun yi kunnen doki ne ci 1-1 a birnin Alexandria a kasar Masar, yayin da kuma a karawa ta biyu Al Ahly ta bi Esperence har gida ta doke t ci 2-1.

Al Ahly da ta lashe gasar ta karbi kudi Dala Miliyan daya da rabi. Kuma yanzu ita ce kungiyar da zata wakilci Nahiyar Afrika a gasar cin kofin zakarun kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Duniya.

Dan wasan kungiyar Chelsea ne ta Ghana Clottey shi ne ya fi kowa zira kwallaye a raga wanda ke da kwallaye 12 a raga.

Akwai Mputu da Samata na TP Mezempe da kuma Aboutrika na Ahly wadanda dukkaninsu suka zira kwallaye 6 a raga.

Sai dan wasan Sunshine ta Najeriya Azuka wanda ya zira kwallaye Biyar.

Kofin Kalubale

A gasar Confedaration kuma a Nahiyar Afrika, an tashi wasa ne ci 2-2 ne tsakanin kungiyar AC Leopards ta Congo Brazzaville da Djoliba ta Mali a karawar farko.

A karshe mako mai zuwa ne za’a yi fafatawar karshe, inda duk kungiyar da ta lashe kofin gasar zata karbi kudi Dala 660.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.