Djoliba da Leopards za su buga wasan karshe a Confederation Cup
Kungiyar Djoliba ta Mali da AC leopards ta Congo Brazzaville su ne kungiyoyin da suka tsallake zuwa buga wasan karshe a gasar kalubale na Nahiyar Afrika bayan sun doke kungiyoyin Sudan guda biyu Al Hilal da Al Merreikh.
Wallafawa ranar:
Djouliba ta doke Al Hilal ne ci 2-0 a birnin Bamako a jiya Lahadi amma sai da aka yi bugun da ga kai sai mai tsaron gida saboda jimillar kwallayen da aka zira a raga.
A ranar Assabar ne kuma aka buga wasa tsakanin Leopards da Merreikh inda aka tashi babu ci, amma Leopard ta samu nasara ne a wasan farko bayan doke Merreikh ci 2-1 a River Nile.
Duk kungiyar da dai ta lashe gasar zata karbi kudi Dala 660,000 inda za’a fara buga wasan karshe a mako mai zuwa a birnin Bamako kafin daga karshe kuma a fitar da gwani a Congo Brazzaville
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu