Isa ga babban shafi
CAN 2013

Masar da Najeriya da Kamaru za su nemi shiga gasar cin kofin Afrika

Kasar Masar da Kamaru da Najeriya da bas u samu shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika ba a Gabon da Equatorial Guinea, a karshen mako ne kasashen za su nemi hucewa a wasannin neman shiga gasar cin kofin Nahiyar da za’a gudanar a Afrika ta Kudu a badi.

Stephen Keshi, Kocin Super Eagles na Najeriya
Stephen Keshi, Kocin Super Eagles na Najeriya
Talla

A yau Juma’a ne kasar Masar zata kara da Afrika ta tsakiya, sai dai za’a gudanar da wasan ne ba tare da ‘Yan kallo ba a birnin Alexandria.

A wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya, da aka gudanar a makwanni biyu da suka gabata masar dai ta lashe wasanninta inda ta doke Guinea ci 3-2 bayan ta lallasa Mozambique. Wanda hakan kuma ke nuna Masar tana da fatar buga gasar cin kofin Duniya a Brazil.

A bara dai Masar bata samu shiga gasar cin kofin Afrika, ba duk da cewa ita ce kasa mai yawan tarihin lashe kofin gasar.

Sai dai mako biyu da suka gabata kasar Afrika ta tsakiya ta lallasa Bostwana ci 2-0 a wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya. Wanda hakan ke nuna Masar sai ta yi da gaske.

Sauran kasashen da zasu haska a karshen mako sun hada da Algeria da Kamaru da Congo Brazzaville da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Habasha da kuma Nigeria.
Algeria da Kamaru da ba su samu shiga gasar ba a bara, Algeria zata kara ne da Gambia, sai Kamaru kuma ta kece raini da Guinea Bissau. A karawar farko dai Kamaru ta doke Guinea Bissau ci 1-0.

Congo Brazzaville kuma zata kara ne da Uganda, sai dai Uganda tasha kashi hannun Congo Brazzaville a karawar farko ci 3-1.

Najeriya kuma zata kara ne da Rwanda, amma a karawar farko kasashen biyu sun tashi ne babu ci.

Jamhuriyyar Benin kuma zata kece raini ne da Habasha. Inda Togo kuma zata fafata da Kenya sai dai Togo tasha kashi ci 2-1 a karawar farko.

A tsarin CAF dai sauran kasashen 16 da suka haska a gasar cin kofin Afrika da aka gudanar a kasashen Gabon da Equatorial Guinea a bana sun tsallake zuwa zagaye na gaba inda za’a sake hada rukunin kasashen a watan Satumba da Octoba. Amma ba tare da Afrika ta kudu ba da zata karbi bakuncin gasar domin ta tsallake kai tsaye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.