Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Libya ta doke Kamaru, Zambia ta lallasa Ghana

‘Yan wasan Kasar Masar sun lallasa Guinea ci 3-2 a birnin Conakry, Kasar Mali kuma ta doke Algeria ci 2-1 a wasan da kasashen biyu suka buga a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, saboda rikicin Siyasa da ake yi a kasar Mali a Wasannin neman shiga gasar cin kofin Kwallon kafa na Duniya.

'Yan wasan kasar Zambia lokacin da suke lashe kofin gasar cin kofin Afrika na bana.
'Yan wasan kasar Zambia lokacin da suke lashe kofin gasar cin kofin Afrika na bana. Reuters
Talla

Bayan dawo wa hutun rabin lokaci ne alkalin wasa ya rage yawan ‘Yan wasan Guinea zuwa 10 bayan ya daga jan kati ga mai tsaron gidan Guinea, Naby Yattara.

A daya bangaren kuma a Rukunin Masar na G, wasa tsakanin Mozambique da Zimbabwe an tashi ne babu ci a birnin Maputo.

Yanzu haka kuma Masar ke jagorancin Rukunin da maki 6 cikin wasannin biyu da aka buga, Sai kasar Guinea da ke bi mata da maki 3.

Kasar Kamaru kuma tasha kashi hannun Libya ci 2-1 a wsan da kasashen suka buga a kasar Tunisia ba tare da ‘Yan kallo ba.

Wasan dai bai yi wa sabon kocin Indomitable Lions dadi ba Denis Lavagne wanda ke kokarin tsallakewa da Kamaru gasar cin kofin Duniya bayan kasa tsallakewa gasar cin kofin Afrika a bana.

Kasar Mali kuma ta doke Algeria ci 2-1 a wasan da kasashen biyu suka buga a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, saboda rikicin da ake yi a kasar Mali.

Kasar Zambia da ta lashe kofin Afrika ta doke Ghana ci 1-0

Jamhuriyyar Nijar tasha kashi hannun Congo Brazzaville da ci 1-0.

Malawi dai da Najeriya sun yi kunnen doki ne ci 1-1

Namibia kuma ta huce kashin da tasha hannun Najeriya inda ta doke Kenya da ci 1-0.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.