Super Eagle na Najeriya sun doke Namibia
‘Yan wasan Super Eagle na Najeriya sun samu nasarar doke ‘Yan wasan Brave Warriors na Namibia da ci daya mai ban haushi a birnin Calabar. Ike Uche da ke taka kwallo a Spain ne ya zira wa Najeriya kwallonta a ragar Namibia.
Wallafawa ranar:
Yawancin ‘Yan wasan da suka taka kwallo matasa ne kodayake akwai John Utaka na Montpellier ta Faransa cikin tawagar ta Super Eagle.
Namibia sai ta sake kara kwazo domin a ranar Assabar zata kara da Kenya Bayan ta sha kashi a Najeriya.
A ranar Assabar, 'Yan wasan Sudan sun lallasa Zambia mai rike da kofin Afrika ci 2-0.
Kasar Jamhuriyyar Benin kuma ta doke Mali ci 1-0.
Wasa tsakanin Uganda da Angola, sun yi kunnen doki ne ci 1-1. Togo da Libya suka yi kunnen doki 1-1.
Wasa tsakanin Jamhuriyyar Nijar da Gabon, an tashi ne babu ci a birnin Yamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu