Kamaru da Senegal sun samu nasara a wasannin sada zumunci
Kasar Kamaru da Senegal sun samu nasarar lashe wasannin sada zumunci da aka gudanar a karshen mako kafin fara buga wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya a watan Yuni.
Wallafawa ranar:
Senegal ta doke Morocco ne ci 1-0, Mousa Konate ne ya zirawa Senegal kwallonta a ragar Morocco.
A faransa kuma Kasar Kamaru ta lallasa Guinea ci 2-1.
Jamhuriyyar Nijar kuma tasha kashi ne hannun Algeria ci 3-0, kamar yadda Saliyo tasha kashi hannun Jordan.
Amma wasa tsakanin Burkina Faso da jamhuriyyar Benin an tashi ne ci 2-2.
Wasa tsakanin Mozambique da Nimibia a kasar Jamus an tashi ne babu ci 0-0.
Haka ma wasa tsakanin Tanzania da Malawi a Dar es Salam an tashi ne babu ci 0-0.
A ranar 1 ga watan Yuni ne kasashen Afrika zasu buga wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya da za’a gudanar a shekarar 2014. A tsakiyar watan ne kuma kasashen zasu buga wasannin neman shiga gasar cin kofin Afrika da za’a gudanar a badi.
Kasar Kamaru dai zata kwashe makwanni uku a jere tana buga wasa inda zata kara da Jamhuriyyar Demokradiyar Congo da Libya a wasannin neman shiga gasar cin kofin Duniya sai kuma wasa tsakanin Kamaru da Guinea Bissau a wasannin neman shiga gasar cin kofin Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu