Isa ga babban shafi

Canada ta yi bankwana da tsohon Firaminista Brian Mulroney

Ministoci da ’yan kasuwa da manyan mashahuran kasar Canada sun hallara a birnin Montreal a yau Asabar wajen jana’izar Brian Mulroney, daya daga cikin Firaministan kasar da suka yi tasiri a shekarun baya-bayan nan, wanda ya rasu a karshen watan Fabrairu yana da shekaru 84 a duniya.

Tutar kasar Canada
Tutar kasar Canada Getty Images via AFP - CHRIS JACKSON
Talla

Akwatin gawar Brian Mulroney, wanda aka lullube da tutar Canada, ya isa Notre-Dame Basilica tare da rakiyar ‘yan sandan fadar masarautar Royal Canadian Mounted, da sojoji da kuma dangi.

A cikin 'yan kwanakin nan, 'yan kasar Canada sun sami damar ba shi girma a Ottawa da kuma Montreal.

Firaminista Justin Trudeau ya ce Brian Mulroney "ya kaunaci wannan kasa da dukan zuciyarsa."

Kuma ba wai kawai yana son Canada a cikin ma'ana ba. Yana son mutanen Canada.

Tsohon Firaminista Brian Mulroney
Tsohon Firaminista Brian Mulroney POOL/AFP

Brian Mulroney ya bar tarihin siyasar Canada a cikin 1980, yana yin kyakkyawar kusanci tare da Amurka na Ronald Reagan wanda ya kai ga rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya ta 'yanci ta tarihi da Amurka, daga baya ya mika zuwa Mexico.

Mai buri da fara'a Brian Mulroney ya kasance manajan kasuwanci kafin shiga siyasa.

Taron kasashen G7 a shekara na 1989 tare da halartar  shugabani da suka hada da  Jacques Delors, Ciriaco de Mita, Helmut Kohl, Georges Bush, François Mitterrand, Margaret Thatcher, Brian Mulroney et Sosuke Uno
Taron kasashen G7 a shekara na 1989 tare da halartar shugabani da suka hada da Jacques Delors, Ciriaco de Mita, Helmut Kohl, Georges Bush, François Mitterrand, Margaret Thatcher, Brian Mulroney et Sosuke Uno © Ullstein Bild Roger-Viollet

Bayan da ya zama firaministan kasar, ya yi ta jin muryarsa a duniya, kuma musamman ma ya jagoranci tuhumar da ake yi wa gwamnatin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, abin da ya harzuka takwararsa na Burtaniya, Margaret Thatcher a cikin lamarin.

"Babu wanda zai iya ba da jawabi kamar mahaifina," in ji 'yarsa Caroline Mulroney, wacce ta fara magana a jana'izar.

A karshen bikin, jikar tsohuwar Firaminista, ta rera wakar Yves Montand da aka sani da "Mais qu'est-ce que j'ai" waƙar da Brian Mulroney kakanta ya fi so".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.