Isa ga babban shafi

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taro a kan rikicin Haiti

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa a Larabar nan a kan rikicin da ke aukuwa a Haiti, inda kungiyoyin ‘yan daba ke brazanar barkewar yakin basasa har sai fira ministan kasar, Ariel Henry ya sauka daga kan mukaminsa.

Gidan yarin birnin Port Au Prince da 'yaan daba suka kona.
Gidan yarin birnin Port Au Prince da 'yaan daba suka kona. AP - Odelyn Joseph
Talla

Kungiyoyin ‘yan daban da ke da iko da wasu yankunan kasar sun sanar da aniyarsa ta kawo karshen mulkin Ariel Henry a rana Alhamis, inda suka kai hare-hare a filin tashi da saukar jiragen saman a birnin Port-au-Prince, gidan yari, ofisoshin ‘yan sanda da sauran mahimman wurare.

A ranar Talata, babban jagoran ‘yan daba a kasar ta Haiti, Jimmy Cherizier, wanda ake wa inkiya da ‘Barbecue’, ya yi kashedin cewa rikicin da ke faruwa a kasar zai kawo kisan kare dangi idan fira ministan kasar bai sauka ba, kuma majalisar Dinkin Duniya ta ci gaba da mara masa baya.

Kamata ya yi Henry, wanda ke jan ragamar mulkin kasar tun bayan kisan gilllar da aka wa shugaba Jovenel Moise a shekarar 2021 ya sauka a watan Fabrairu, amma a maimakon haka ya amince da wata hadaka da ‘yan adawa har zuwa lokacin da za a gudanar da wani zabe.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 15 ne suka arce daga sassan birnin Port-au-Prince da rikici ya  tsananta, sai dai ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu ba.

Sai dai a yayin da ake ci gaba da wannan rikici, Henry ya gaza komawa gida.

Yana can kasar Kenya a kokarin da ya ke na ganin an tura hadakar ‘yan sandan kasa da kasa a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya don taimakawa wajen maido da kasarsa hayyacinta, sai kwatsam aka fara batun hambarar da shi daga kan mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.