Isa ga babban shafi
Cuba - Amurka

Muguntar Amurka ce ta janyo mana matsalar cikin gida - Cuba

Cuba ta bayyana matakin Amurka na kuntatawa tattalin arzikinta a matsayin dalilin da ya janyo gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnatin Kwamunisancin kasar, yayin da shugaba Joe Biden ya goyi bayan kirye-kirayen kawo karshen zaluntar al’ummar kasar.

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Cuba a birnin Havana. 11/7/2021.
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Cuba a birnin Havana. 11/7/2021. © YAMIL LAGE / AFP
Talla

Dubban mutanen Cuba sun shiga zanga-zangar adawa da gwamnatin Cuba a karshen mako, cikin rera wake-waken tofin alatsine kan gwamnati, yayin da shugaban kasar Miguel Diaz-Canel ya zaburar da magoya bayansa da su yi fito-na-fito da masu yi masa bore.

Zanga-zangar ta warwatsu zuwa biraen kasar wadda ke fama da matsanancin tabarbarewar tattalin arziki mafi muni cikin shekaru 30, lamarin da ya haddasa karancin wutar lantarki da kuma abinci.

Wani mutum da 'yan sandan Cuba suka kama yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Miguel Diaz-Canel.
Wani mutum da 'yan sandan Cuba suka kama yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Miguel Diaz-Canel. YAMIL LAGE AFP

Jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar, sannan sun cafke mutane 10 baya ga dukan masu boren da bulalar roba kamar yadda wani wakilin AFP ya ganewa idonsa.

Shugaba Diaz-Canel ya zargi Amurka da yin amfani da matsin tattalin arziki domin haddasa tashin hankali a kasar.

Tun dai shekarar 1962 Cuba ke dandana azabar takunkuman karya tattalin arziki da Amurka ta lafta mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.