Isa ga babban shafi
EU-MDD

Eu ta bukaci goyon bayan MDD akan Matsalar bakin Haure

Shugabar ofishin kare manufofin ketare na kungiyar kasashen Turai EU, Frederica Mogherini, ta ce gaggauta kawo karshen yadda ake samun kwararar bakin haure zuwa Turai, shi ne babban abin da ke gabansu. Domin kare rayukan duban mutane da ke mutuwa a kokarinsu na tsalakawa turai.

Shugabar kungiyar kasashen turai Federica Mogherini
Shugabar kungiyar kasashen turai Federica Mogherini REUTERS/Michael Dalder
Talla

Federica Mogherini wadda ke gabatar da jawabi a gaban wakilan kasashen 15 mambobi a kwamitin sulhu na MDD, ta ce Turai ta damu matuka a game da yadda ake samun karuwar bakin haure da kuma asarar rayukan a koda yaushe.

Matsalar da Mogherini ta ce ba za su iya shawo kai su kadai ba, sai da haddin kan duniya baki daya.

Wakilan MDD da na EU, na aiki da kasar italy akan wani daftari, da zai bada damar yin amfani da wasu tsare-tsare akan batun bakin haure, da masu safara su.

A cikin shekarar na kadai, Tekun meditterenean ya lakume rayukan mutane akalla dubu 1800.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.