Isa ga babban shafi

Yau Strauss-Khan zai bayyana a gaban wata kotun Faransa

A yau littini ne tsohon Shugaban Asusun bada lamuni na duniya IMF, wato Dominique Strauss-Khan, zai sake gurfana gaban wata kotun kasar Faransa bisa zargin da ake masa na muamala da karuwai.Tun shekaru 4 da suka gabata ne aka dama lissafin Dominique Strauss-Khan na zama shugaban Faransa da ake ta yadawa a lokacin.A wancan lokaci ne aka kama shi a birnin New York na kasar Amurka, inda ake zarginsa da neman yiwa wata ma’aikaciyar Otel din daya sauka fyade.A wannan karon ana zarginsa ne da laifin shiga wata kungiyar dake dillancin karuwai zuwa kasashen da mabukaci ke so.Dominique Strauss-Khan mai shekaru 64 ya rike mukamin Ministan kudi a Faransa kafin likkafa taci gaba ya zama shugaban Bankin bada lamuni na duniya IMF, kafin a sauke shi babu shiri saboda laifin neman yin fyade da ake zargin sa.A yau littin ne zai gurfana gaban kotun, dake yankin Lille tare da wasu mutanen 13, inda ake zarginsu da laifin zinace-zinace ba kangadoWani bincike da jaridar Le Parison dake Faransa ta gudanar na cewa ba don saboda matsalar neman mata da yayi masa yawa ba, da shine ya dace ya zama shugaban Faransa. 

Dominique Strauss-Khan era acusado de crime e violência sexuais.
Dominique Strauss-Khan era acusado de crime e violência sexuais. REUTERS/Richard Drew/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.