Isa ga babban shafi
Italiya

An ceto bakin haure 700 a tekun Italiya

Kimanin bakin haure 700 ne aka yi nasarar ceto rayuwarsu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya fara nutsewa da su a cikin teku kusa da wani tsibiri a kasar Girka. Rahotanni sun ce bakin hauren sun isa Italiya.

Bakin Haure da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai
Bakin Haure da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai UNHCR
Talla

Wakilin Kamfanin Dillacin labaran Faransa yace Bakin hauren sun isa tashar ruwan Gallipoli a kudancin Italiya a yau Laraba.

Ma’aikatan gaban ruwa Italiya ne dai suka kai dauki da jiragen sama masu saukan Angulu a lokacin da suka sami rahoton neman agaji na gaggawa domin ceto rayuwar ayarin bakin hauren.

Yanzu haka ‘Yan sanda sun kaddamar da bincike akan yadda bakin hauren yawancinsu daga Syria suka samu shiga jirgin ruwan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.