Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Ukraine ta baiwa ‘yan tawaye ‘yanci na wuccin-gadi

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya bayyana mika wani bangare na kasar, wadda ke matsayin tsohuwar Mamba a tarayyar Soviet, ya kasance a karkashin mulkin wuccin-gadi ga ‘yan tawayen masu goyon bayan kasar Rasha. Wannan dai na a kumshe ne a karkashin yarjejeniyar samar da zaman lafiyar da ke tsakanin kasar da kasar Rasha

Lực lượng ly khai thân Nga tại Donetsk. Ảnh chụp ngày 08/09/2014.
Lực lượng ly khai thân Nga tại Donetsk. Ảnh chụp ngày 08/09/2014. Reuters
Talla

Shugaban mai samun goyon bayan kasashen Turai ya gayawa ‘yan Majalisun kasar cewar yin hakan na daga cikin yarjejeniyar samar da zaman lafiya da suka rattabawa Hannu tsakaninsu da ‘yan tawayen kasar masu goyon bayan Rasha a ranar 5 ga Watan Satunmba.

Ikon tafiyar da al’amurran shugabanci na wuccin-gadin da ‘yan tawayen suka samu dai na shekaru 3 ne, kuma a yau Talata ne shugaban ya kuduri aniyar gabatar da bukatar yin hakan a gaban Zauren Majalisar kasar.

Kudurin Dokar dai ya fayyace ‘yancin da al’ummar yankin na gabashin Ukraine ke da shi na amfani da Harshen Rashanci a Hukumominsu, a yankunan Lugansk da Donesk, su kuma gudanar da zaben shugaban kasa da kansu a ran 9 ga Watan Nuwamba.

Hakama Kudurin Dokar ya basu cikakkiyar damar yin kyakkyawar hulda da Makwabtansu da ke cikin kasar Rasha ta fannin Diplomasiyya.

Shugaban kasar kuma ya bukaci Majalisar kasar da ta hanzarta amincewa da kudurin lura da fadan da ake a yankin ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa.

Ya zuwa yanzu dai an kashe akalla mutane 2,700 a fadan kuma wannan ya nuna babbar nasarar da ‘yan tawayen suka samu.

Dam adai kasar Rasha ta fada cewar kassahen Turai ne ke ingiza Ukraine fada da ita kuma sun san hakan ba zata yiyu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.