Ministocin kudin Tarayyar Turai sun goyi bayan shirin taimakawa Cyprus
Ministocin kudi na kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da wani shirin tallafawa kasar Cyprus da kudaden da yawansu ya kai Euro bilyan 10 domin ceto tattalin arzikin kasar da ya shiga hali na tangal-tangal.
Wallafawa ranar:
Matakin da ministocin da kasashen na kungiyar tarayyar Turai suka dauka, shi ne zai sa sauran kasashen kungiyar gabatarwa Majalisun dokokinsu da wannan batu domin tallafa wa kasar ta Cyprus da kudade a cikin shekaru uku masu zuwa, daga cikin kasashen da suke da niyyar yin hakan sun hada da Jamus da kuma Finland.
A karkashin wannan shiri dai, kasashen na nahiyar Turai ne za su bayar Euro bilyan 9, yayin da Asusun Lamuni na Duniya IMF zai samar da bilyan daya. Har ila yau ana kyautata zaton cewa a cikin shekaru 15 zuwa 20 ne wannan shiri zai kai ga yin tasirin kubutar da tattalin arzikin kasar ta Cyprus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu