Isa ga babban shafi
Ukraine

Sauraren karar Yulia Tymoshenko a Ukraine

Daruruan magoya bayan Tsohuwar Firaministan Ukraine, Yulia Tymoshenko sun hada gangami a harabar kotun da ake sauraren kararta a birnin Khariv a yau Litinin, kamar yadda gwamnatin Ukraine ke fuskantar Matsin lamba daga kasashen Turai wadanda ke nuna adawa da hukuncin daurin shekaru Bakwai da aka yanke ma ta tare da cin zarafinta.

Wasu Magoya bayan Tsohuwar Firaministan kasar Ukraine Yulia Tymoshenko
Wasu Magoya bayan Tsohuwar Firaministan kasar Ukraine Yulia Tymoshenko REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

Akwai wakilin kungiyar kasashen Turai da suka halarci zaman kotun da suka hada da tsohon Shugaban kasar Poland Alexander Kwasniewski da tsohon kakakin Majalisar Turai dan kasar Ireland Pat Cox. Amma ana sauraren karar ne ba tare da Tymoshenko ba saboda rashin lafiya.

Daruruwan magoya bayan Tymoshenko ne suka hada gangami tare da yin shelar neman wa tsohuwar Firaministan ‘Yanci.

Sau biyu ne dai ana dage sauraren karar tsohuwar Shugabar saboda rashin lafiyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.