Nijar
Ma’aikatun raya karkara sun shiga yajin aiki a Nijar
Ma'aikatan da ke aiki a ma’aikatun raya karkara a Jamhuriyar Nijar da suka hada malaman gona da kuma likitocin dabbobi, sun soma wani yajin aikin na tsawon kwanaki 3, inda suke neman gwamnati ta cika alkawalin da ta dauka a karkashin wata yarjejeniya da suka kulla da a baya. Ma’aikatan dai sun yi barazanar rike alkaluman na irin ayyukan da suke gudanarwa, wadanda gwamnatin ke bukata domin sanin bukatun al’umma. Daga Damagaram, wakilinmu Ibrahim Malam Chilo ya aiko da Rahoto.
Wallafawa ranar:
Talla
Nijar: Ma’aikatun raya karkara sun shiga yajin aiki a Nijar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu