Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Za a naɗa dan Kwankwaso kwamishina a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa wa Majalisar Dokokin Kano sunan ɗan tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso domin tantancewa a matsayin kwamishina.

Rabi'u Musa Kwankwaso
Rabi'u Musa Kwankwaso © Premiumtimes
Talla

 

Mustapha Rabiu Musa na daga cikin sunayen mutum huɗu da gwamnan ya miƙa wa majalisar domin tantance naɗin muƙaminsu a matsayin kwamishinoni.

Sauran sunayen waɗanda aka miƙa wa majalisar sun haɗa da tsohon Kwamishinan Filaye da Saliyo da aka kora, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, Alhaji Abdul-Jabbar Umar Garko da Shehu Usman Aliyu Karaye.

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Majalisar Dokokin Kano, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar a wannan Talatar.

Mustapha Rabi'u Kwankwaso
Mustapha Rabi'u Kwankwaso © Aminiya

Shawai ya ce ana sa ran za a tantance naɗin muƙaminsu a ranar Talata, 2 ga watan Afrilun 2024.

 

Sanarwar ta kuma ambato Kakakin Majalisar, Jibrin Ismail Falgore na cewa miƙa sunayen kwamishinonin domin tantancewa na zuwa ne a daidai kan gabar da Gwamnan ya miƙa buƙatar kafa wasu sabbin ma’aikatu a Kano.

A ƙunshin wasiƙar da Honarabul Falgore ya karanta a zauren majalisar, ya ce sabbin ma’aikatun da za a kafa sun haɗa da Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Yaƙi da Fatara, Ma’aikatar Albarkatun Kasa, Ma’aikatar Makamashi da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida da Ayyuka na Musamman.

A cewar Honarabul Falgore, buƙatar kafa sabbin ma’aikatun na da nasaba ne da ƙudirin Gwamnan na inganta ƙwazo a harkokin jagoranci.

Ya bayyana cewa Gwamnan ya buƙaci kafa sabbin ma’aikatun ne waɗanda za su taka rawar gani wajen inganta harkokin tattalin arziki, zamantakewa da samar da shugabanci na gari tare da sanya jihar a wani matsayi na ci gaba mai dorewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.