Isa ga babban shafi
MIYAGUN KWAYOYI

Zamu taimakawa Najeriya dakile amfani da miyagun kwayoyi - Amina Mohammed

Najeriya – Majalisar dinkin duniya tayi alkawarin taimakawa Najeriya wajen ganin ta samu nasarar yaki da shan kwayoyi da kuma haramta safarar su zuwa kasashen ketare, a daidai lokacin da hukumar ta kama mutane sama da dubu 48 a karkashin jagorancin Janar Muhammadu Buba Marwa.

Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Amina Muhammed lokacin da ta ziyarci shugaban hukumar NDLEA Janar Muhammadu Buba Marwa
Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya Amina Muhammed lokacin da ta ziyarci shugaban hukumar NDLEA Janar Muhammadu Buba Marwa © NDLEA
Talla

Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Amina Muhammed ce ta sanar da haka lokacin da ta ziyarci shugaban hukumar NDLEA Janar Muhammadu Buba Marwa mai ritaya a ofishin hukumar dake Abuja.

Amina Muhammed tare da rakiyar shugaban ofishin Majalisar dake Najeriya, Mohammed Malick tace a shirye suke su tallafawa Najeriya wajen ganin ta samu gagarumar nasarar shawo kan illar da amfani da miyagun kwayoyin keyi a tsakanin al'umma.

Amina Muhammed tare da Janar Buba Marwa na NDLEA da kuma jagoran hukumomin Majalisar dinkin duniya dake Najeriya Muhammed Malick
Amina Muhammed tare da Janar Buba Marwa na NDLEA da kuma jagoran hukumomin Majalisar dinkin duniya dake Najeriya Muhammed Malick © NDLEA

Sakatariyar tace tattaunawar da suka yi da Janar Marwa ta dada tabbatar da bukatar hadin gwuiwa wajen ganin an tinkari matsalar wadda ke dada kamari a tsakanin al'umma, yayin da ta bayyana aniyarsu ta yin aiki tare da hukumomi irin na Najeriyar wajen basu tallafin da ake bukata.

Muhammad ta kuma jinjinawa shugaban hukumar NDLEA saboda rawar da ma'aikatansa ke takawa da kuma karin kaimin da aka samu wajen gudanar da ayyukan su.

Sakatariyar tace lokacin da suke tasowa sun kalli irin jagorancin da Janar Marwa ya bayar a bangaren soji, wanda kuma yanzu haka ke gudana a hukumar ta NDLEA, yayin da ta sake jaddada muhimmancin ceto Najeriya daga wannan matsalar da ke yiwa matasa matukar illa.

Shugaban NDLEA Janar Marwa ya yaba da ziyarar wadda ya bayyana ta a matsayin mafi girma da aka samu daga Majalisar Dinkin Duniya, yayin da yace zai dada bai wa jami'an sa kwarin gwuiwar ci gaba da gudanar da ayyukan su.

Marwa ya kuma yabawa Amina Muhammed a kan wakilcin Najeriya da take yi a Majalisar dinkin duniya da kuma irin gudumawar da take bayarwa wanda ya zama abin koyi, a daidai lokacin da yake bayyana muhimmancin taimakawa hukumarsa shawo kan wannan matsala ta amfani da kwayoyi da kuma safarar su.

Shugaban hukumar yace suna samun nasarar dakile yadda shan kwayar da safarar ta ke yiwa bangaren kula da lafiyar jama'a da kuma kasa barazana, bayan ya bayyana irin nasarorin da suke samu.

Marwa yace daga kama aikinsa a hukumar zuwa yanzu, sun yi nasarar kama mutane dubu 48 da 157 cikin su harda fitattun dillalai 46, yayin da tuni kotu ta yanke hukunci a kan dubu 8 da 350, kuma an kwace kwayar da ta kai tan dubu 7 da 500 da kuma lalata eka dubu 1 da 057 da ake noma tabar wiwi.

Sanarwar da Daraktan yada labaran hukumar Femi Babafemi ya rabawa manema labarai tace NDLEA tayi nasarar kula da wadanda kwayar ta yiwa illa da kuma dawo da su cikin hayyacin su da yawan su ya kai dubu 29 da 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.