Anyi gangamin sharar makabartar wadanda suka mutu da cutar Ebola a Liberia
Dumbin mutane sun yi gangamin share kaburbura a makabartar da aka shimfide wadanda cutar Ebola ta kashe mafi girma a Laberiya a ranar Laraba, yayin da kasar ke gab da cika shekaru 10 da fuskantar iftila’in cutar.
Wallafawa ranar:
Kasar da ke yammacin Afirka ta yi fama da cutar Ebola ce wacce ta barke a tsakanin shekarar 2014 zuwa 2016, ta kuma kashe mutane 4,810 a Laberiya kadai.
An tabbatar da bullar cutar ta farko a kasar ce a ranar 30 ga Maris, 2014, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Fasto Charles Brown, wanda ya kafa gidan marayu ga yaran da iyayensu suka mutu a lokacin cutar Ebola ya ce "Yana da matukar wahala a gare mu.
Makabartar Disco Hill da ke kudu da Monrovia babban birnin kasar an yi ta ne da farko don daukar wadanda cutar Ebola ta kashe, amma a yanzu haka tana dauke da gawarwakin wadanda suka mutu yayin barkewar cutar ta Covid-19.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu