An gano wasu mutane dauke da Ebola a Guinea
Gwamnatin kasar Guinea ta bayyana cewa an samu mutane biyu dauke da cutar Ebola bayan an yi musu gwaji.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne ‘yan sa’oi da hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, babu sauran cutar a kasar Saliyo mai makwabtaka da Guinea.
Wani jami’in gwamnatin kasar ya ce, mutanen da suka kamu da cutar mazauna kauyen Korokpara ne, inda aka samu mutane uku 'yan gida daya da suka rasa rayukansu a 'yan makwannin da suka shude bayan sun yi ta amai da gudawa.
An yi amanna cewa, cutar ta Ebola ta fara bulla ne a kasar Guinea yayin da ta kashe sama da mutane dubu 11 da 300 tun bayan barkewarta a shekarar 2013 a kasashen Liberia da Saliyo da Guinea.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu