Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta ce likitoci sama da dubu 16 ne suka tsere daga kasar don aiki a ketare

Gwamnatin Najeriya ta ce kasar ta rasa likitoci dubu 16 cikin shekaru biyar, saboda yadda likitocin ke guduwa don aiki a kasashen ketare.

Wasu daga cikin likitocin Najeriya
Wasu daga cikin likitocin Najeriya © Daily Trust
Talla

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake samun karuwar likitocin da ke tsallake Najeriya zuwa ketare don aiki a can, bisa hujjar rashin kyawun yanayin aiki.

Da yake bayani a kafar talabijin ta Channels da ke kasar, ministan lafiya Farfesa Ali Pate ya ce likitoci dubu 55 ne kachal ke kulawa da marasa lafiyan da ke Najeriya mai yawan mutane sama da miliyan 200.

Farfesa Pate ya nuna takaicin sa kan yadda wannan matsala ke dulmiyar da Najeriya cikin karancin kwararrun likitoci da ke kulawa da cututtuka masu sarkakiya, sai dai ya jadadda cewa gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen shawo kan wannan matsala.

Yawan jami’an lafiya a Najeriya da suka hadar da likitoci, ungozoma, malaman jinya, masu bada magunguna da jami’an gwaje-gwajen cututtuka da samfurin jini bai zarta dubu 300 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.