Isa ga babban shafi

Sojin Najeriya sun kwato makamai da mashina a hannun 'yan bindigar Kaduna

Rundunar Sojin Najeriya ta 1 ta sanar da nasarar kwato tarin makamai da mashina daga hannun 'yan bindigar daji a jihar Kaduna ta arewacin kasar yayin sumamen da suka kai wata maboyarsu a cikin daji.

Sojojin Najeriya a Kaduna.
Sojojin Najeriya a Kaduna. AP
Talla

Wata sanarwar Rundunar dauke da sa hannun mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar, Laftanar Kanal Musa Yahaya ce ke sanar da wannan nasara a sumamen wanda sojojin suka kai jiya Talata.

Musa ya ce bayan samun wasu bayanan sirri da kuma yunkurin da rundunar ke yi na ganin ta kakkabe 'yan bindiga daga dazukan jihar kaduna, dakarun rundunar da hadin gwuiwa na ''Yan bangar jihar sun yi wa 'yan bindigar kwanton bauna a yankin Dogon Dawa zuwa Damari, ko da ya ke 'yan bindigar sun tsere cikin tsakar daji bayan luguden wutar da suka sha.

A cewar jami'in  " Bayan bincike dajin sai dakarun mu su ka gano bindigogin Fistil kirar Bareta da Ak 47 da kuma tarin alburusai."

Haka zalika, dakarun rundunar da ke kula da kwanar mutuwa a karamar hukumar  Birnin Gwari bayan samun bayanan sirrin cewa 'yan bindiga sun shigo yankin, nan ta ke, Sojoji  suka tunkaresu suka kuma tarwatsa su, 'yan bindigan dai sun tsere bayan sun fahimci cewa an fi karfin su.

" Anan kuma dakarun mu sun kwato mashina guda uku."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.