Isa ga babban shafi
labarin aminiya

Magidantan da ’yan bindiga suka kashe a Masallaci a Kaduna sun bar marayu 61

Hudu daga cikin mutanen da ’yan bindiga suka kashe a masallaci a kauyen Saya-Saya na Karamar Hukumar Ikara a Jihar Kaduna sun bar marayu da zawarawa 61.

Hare-hren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya
Hare-hren 'yan bindiga sun salwantar da rayuka da dama a arewacin Najeriya Jakarta Globe
Talla

An dai kai harin ne kan mutanen lokacin da suke tsaka da sallar Isha a masallaci, inda aka kashe mutum biyar, hudu daga cikinsu kuma magidanta ne, sannan aka jikkata wasu.

Wani manomi kuma ɗan kasuwa a kauyen, Ya’u Ibrahim, wanda daya ne daga cikin wadanda aka kashe ya rasu ya bar ’ya’ya 20 da mata biyu.

Sauran sun hada da wani Kwamandan ’yan sa-kai wanda aka yi ittifakin shi suka yi fako a harin mai suna Malam Isiyaka, wanda ya rasu ya bar ’ya’ya 17 da mata uku.

Shi kuwa Yunusa Nuhu ya bar yara 14 da mata biyu, yayin da Malam Adamu Maidara ya bar yara 10.

A cewar wani shugaban al’umma a yankin, Malam Dan Asabe Saya-Saya yayin zantawarsa da Aminiya, ya bayyana harin a matsayin abin takaici.

Sai dai ya ce mutum na biyar da aka kashe mai suna Mustapha Sale mai kimanin shekara 25, shi kadai ne ba shi da mata a cikinsu.

“Kamar yadda ka sani, dukkan mutum biyar din da aka kashe ’yan wannan kauyen ne, amma ragowar daga makwabtan garuruwa suke. Sai dai hudu daga cikin wadanda aka kashe a kauyenmu na da sun bar ’ya’ya da zawarwa 61,” in ji shi.

Dan Asabe ya ce shi kuma mutum na biyar din, tuni har an riga an yi masa baiko, ana shirye-shiryen sanya masa ranar aure ne.

Sai dai ya ce iyalan mutanen na cikin tsananin bukatar taimako saboda da su suka dogara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.