Isa ga babban shafi

Najeriya: Gwamnatin Kaduna ta dauki sabbin ‘yan banga dubu 7 don yakar ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Kaduna dake Najeriya ta sanar da daukar sabbin matasa kimanin dubu 7 amatsayin ‘yan banga domin taimakawa jami’an tsaro kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a fadin jihar.

Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani da sabbin 'yan banga da aka diba.02/09/23
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani da sabbin 'yan banga da aka diba.02/09/23 © sen. Uba Sani X handle
Talla

Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya tabbar da matakin yayin bukin kaddamar da bada horo ga matasan da yammacin wannan Asabar a kwalejin horas da ‘yan sanda dake jihar, inda ya ce an zakulo matasan dubu 7 ne daga daukacin kananan hukumomin jihar, domin taimaka masa wajen cika alkawarin da ya dauka da kawo karshen matsalolin rashin tsaro dake addabar jihar.

Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani yayin bukin kaddamar da horon sabbin 'yan banga a jihar. 02/09/23
Gwamnan jihar Kaduna Sen. Uba Sani yayin bukin kaddamar da horon sabbin 'yan banga a jihar. 02/09/23 © Sen. Uba Sani X handle

Kaddamar da Shirin horon ‘yan bangar ne sa’o’I kalilin bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari wani masallaci a Ikara dake jihar tare da kashe wasu masallata.

A cewar Gwamnan, gwamnatinsa zata maida hankali wajen kara yawan jami’an na Vijilantin na (KADVS) da kuma inganta daukacin hanyoyin saukaka ayyukansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.