Isa ga babban shafi

'Yan sanda sun kama wadanda suka yi garkuwa da daliban Jami'ar Greenfield

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargin suna da hannu wajen sace dalibai daga wata jami’a da ke arewacin kasar a shekarar da ta gabata, daya daga cikin sata da garkuwa da dalibai suka fi daukar hankali a kasar.

Wata motar soji bayan isa jami'ar Greenfield inda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna a Najeriya, ranar 21 ga Afrilu, 2021.
Wata motar soji bayan isa jami'ar Greenfield inda wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai a Kaduna a Najeriya, ranar 21 ga Afrilu, 2021. © REUTERS/Bosan Yakusak
Talla

A ranar 20 ga Afrilun shekarar 2021, wasu ‘yan bindiga suka kashe wani ma’aikaci a yayin da suka kai farmaki jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin kasar, inda suka sace dalibai kusan 20.

‘Yan bindigar sun kashe biyar daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su cikin kwanaki kadan don tilastawa iyalai da gwamnati biyan kudin fansa, kafin daga bisani su saki ragowar dalibai goma sha hudu bayan kwanaki 40 a tsare.

Da yammacin ranar Larabar nan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane biyu da suka hada Aminu Lawal, wanda aka fi sani da Kano, da kuma Murtala Dawu, wanda aka fi sani da Mugala – wadanda ke da hannu a wasu laifuka da dama na satar mutane.

Cikin sanarwar da ya fitar, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriyar Olumuyiwa Adejobi ya ce dukkanin mutanen biyu, sun amsa laifin yin garkuwa da daliban jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna, da kuma kashe biyar daga cikinsu kafin a biya su kudin fansa, su kuma su saki sauran.

Kakakin ‘yan sandan ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan bincike.

Kimanin dalibai dubu 1,500 'yan bindiga suka sace a arewacin Najeriya

Kungiyoyin masu aikata laifuka dauke da muggan makamai sun zama barazanar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar Najeriya, inda suke afkawa kauyuka da aikata laifukan fashi da makami da kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta nuna cewar, bayan da  ‘yan bindigar suka mayar da hankalinsu ga makarantun karkara da jami’o’i, sun sace yara ‘yan makaranta kimanin 1,500 a shekarar da ta gabata, daga cikin hare-hare sau 20 da ‘yan ta’addan suka kaiwa makarantu a yankin arewacin Najeriya, inda dalibai 16 suka rasa rayukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.