Isa ga babban shafi
Najeriya - Kaduna

Halin da ake ciki a Kaduna bayan sace dalibai fiye da 100

Gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wasu makarantu 13 dake yankunan da ka iya fuskantar farmakin 'yan bindiga.

Taswirar jihar Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna. © Kada News Magazine
Talla

Matakin dai ya biyo bayan harin da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai kan wata makarantar Sakandare dake karamar hukumar Chikun inda suka kwashe dalibai akalla 140.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun afkawa makarantar sakandaren ce da ake kira ‘Bethel Secondary School’ cikin harbin kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su kwashe daliban ta su gudu da su.

Wakilinmu a Kaduna Aminu Sani Sado ya aiko mana da rahoto kan halin da ake ciki.

Rahoton Aminu Sani Sado kan halin da ake ciki a Kaduna bayan sace dalibai da dama a Chikun

Rahoton Aminu Sani Sado kan halin da ake ciki a Kaduna bayan sace dalibai da dama a Chikun

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.