Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun sake kashe 2 daga cikin daliban jami'ar Greenfield a Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya ta ce 'yan bindigar da suka sace daliban Jami’ar Greenfield mai zaman kan ta sun sake kashe biyu daga cikin su, bayan guda 3 da suka kashe a makon jiya.

Wani jami'in dan sanda a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya.
Wani jami'in dan sanda a jihar Kaduna dake arewacin Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Samuel Aruwan ya sanar da kisan a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai, inda ya ke cewa jami’an tsaro sun samo gawarwakin biyu daga cikin daliban da aka kashe yau litinin.

Aruwan ya ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana bacin ran sa da kisan da aka yi wa daliban wadanda ke neman ilimi domin gyara makomar rayuwar su.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta aike da sakon ta’aziya ga iyayen daliban da kuma shugabannin jami’ar dangane da wannan rashi.

Su dai 'yan bindigar sun bukaci a biya su diyyar naira miliyan 800 domin sakin daliban, yayin da gwamnatin jihar Kaduna ta ce har yanzu tana kan bakarta na kin tattaunawa ko kuma biyan diyya ga masu garkuwa da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.