Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

An katse layukan sadarwa a wasu yankunan Kaduna

A Najeriya, Gwamnatin Jihar Kaduna ta soke amfani da Babura, sannan kuma ta takaita wuraren da Babura masu kafa uku za su rika shiga, domin kawo karshen rashin tsaro da ke neman wuce gona da iri.

Manyan turakun kamfanonin sadarwa a Najeriya.
Manyan turakun kamfanonin sadarwa a Najeriya. © Nairametics
Talla

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka, inda yace matakan haramcin da zai dauki tsawon watanni uku zai fara aiki daga ranar Alhamis 30 ga watan Satunba na wannan shekarar 2021 da muke ciki. Inda aka takaita babura masu taya uku aiki daga karfe 6 na safe zuwa 7 na yamma. 

Aruwan yace tuni gwamnatin tarayya ta toshe layukan sadarwa a wasu yankuna jihar, bisa bukatan hukumomin Kaduna har illa masha Allahu.

Cikin matakan da gwamnatin jihar Kadunan ta dauka sun hada harda mallakar makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.