Isa ga babban shafi
Najeriya - 'Yan bindiga

'Yan bindiga a Kaduna sun saki daliban makarantar Bethel Baptist 32

Rahotanni daga Najeriya na cewa karin dalibai 32 na makarantar Bethel Baptist High School dake Kaduna, suka samun 'yanci daga hannun 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Allon makarantar Bethel Baptist da 'yan bindiga suka sacewa dalibai 121 a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.
Allon makarantar Bethel Baptist da 'yan bindiga suka sacewa dalibai 121 a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna. © AP
Talla

Joseph Hayab, Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ya tabbatar da sakin daliban a ranar Juma’a.

Hayab, wanda ya ce tuni aka hada daliban da iyayensu, bai yi cikakken bayani ba dangane da yanayin sakinsu ba. To said ai har yanzu akwai sauran daliban makarantar 31 da suka saura a hannun ‘yan bindigar.

Daliban Tegina

Wannan ci gaban na zuwa ne kwana guda bayan da daliban makarantar Salihu Tanko Islmammiya da ke Tegina a jihar Neja suka samu 'yanci bayan shafe kwanaki 88 a hannun masu garkuwa da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.