Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna-'Yan bindiga

'Yan bindiga 9 sun mutu sakamakon rikici a tsakaninsu

Gwamnatin jihar Kaduna a Najeriya ta ce ‘yan bindiga 9 ne suka mutu sakamakon wani kazamin rikici da ya barke a tsakaninsu  a wani kauye da ke karamar hukumar Giwa ta jihar.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Samuel Aruwan, wanda shine kwamishinan  tsaro da harkokin cikin gida a jihar ya ce bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa wani kasurgumin dan bindiga da ake wa inkiya da  Godon Mota ne ya kutsa da shi da tawagarsa kauyen Garke a Larabar da ta gabata, kuma nan ne rikici tsakanin abokan hamayyar ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda 9.

Aruwan ya ce har yanzu ba a  tantance ummul’aba’isin rikicin nasu ba, amma ana zargin ba zai rasa nasaba da rabon kudin fansa da suka tara ba.

Jihar kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na fama da ayyukan ‘yan bindiga da masu satar mutane don karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.