Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna-'Yan Bindiga

'Yan bindiga sun kashe mutane 3 tare da jikkata da dama a Kaduna

Mutane 3 sun mutu yayin  da dama suka jikkata a wani hari da aka kai karamar hukumar Zangon Kataf a da ke jihar Kaduna a Najeriya.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i Twitter@GovKaduna
Talla

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya tabbatar da aukuwar lamarin  a wata sanarwa da ya fitar a Juma’a.

Aruwan ya ce sun samu labarin cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a kauyukan Machun da Manuka inda suka kashe mutane uku tare da raunata da dama.

Ya ce  ba a fayyace adadin wadanda suka samu rauni ba, amma suna nan suna karbar magani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.